*Meh yasa Fintiri yake kwaikwayon ayyukanta
*Hasashe ya bata kashi 70 na tazaran maki zuwaga nasara
*Yadda jin tsoronta ya ingiza Fintiri yake gudun wuce sa’a da kuma sayan kuri’u a fakaice
*Ainihin dalilan da suka sa Binani ke morewa daga samun goyon bayan mabiyanta
Daga: DAHIRU SANI
Sanata Aishatu Dahiru Ahmed Binani ta gama kintsawa tsab domin shiga gidan gomnati dake Dougirei a matsayin farkon zababbiyar gomna mace a Nigeria a ranar 18 ga watan Maris din 2023 a jahar Adamawa da akewa lakabi da kasar kyawawa.
Duba da yanayin jihan a yanzu kai tsaye mutum zai iya cewa saura yan kwanaki ne kafin Binani ta shiga gidan gomnati a matsayinta na wacce zata gaji gomna Ahmadu Umaru Fintiri muddin sahihan kuri’u ne ke kai mutum ga nasara.
Banda tsohon gomna Murtala Nyako babu wani dan takaran gomna daya samu gagarumin goyon bayan al’uma irin wadda Binani ta samu wadda hakan yasa da dama daga cikin jama’a sunyi imanin cewa a sauwake Binani zata shiga cikin gidan gomnati dake Dougirei.
Cibiyar bincike mai zaman kanta ta Democracy Watch Network (DWN) ita ce ta baiyana irin karbuwarta a wani gagarumin aikin jin ra’ayoyin jama’a data gudanar a jahan nan.
A cewar Mr. Stephen Godwin shugaban bincike da tsare-tsare na DWN Binani zatayi nasara ne da kaso 70 wadda hakan zai bata daman kafa tarihi a Jahan.
Yace ra’ayoyin a kalla mutum 500,000 akaji a tsakanin kananan hukumomi 21 tare da samun tabbacin kaso 95.
Yace matasa, mata da kuma masu larurar nakasa sune sukafi yin amanna da takaran tata duba da yadda kashi 80 daga ciki sukayi na’am da manufofinta suna mai tsammanin samun rayuwa mai inganci da samun kayakin tallafi wadda ya ceto iyalai da dama daga fadawa kangin talauci muddin Binani ta samu darewa kan kujeran iko a jahar Adamawa.
Yace ko shakka babu jajirtacciya kuma hazikan yar takaran na APC sanata Aishatu Binani mace mai kamar maza wacce tayi kaurin suna wurin tallafawa al’uma zata doke abokan karawarta musamman ma gomna mai ci a ko wani lokaci.
Tabbas sanata Binani zata girbe abunda ta shuka na gudanar da shugabanci mai nagarta da tallafawa jama’a inda aka ga ta karya lagon wadanda basu tabuka abun azo a gani idan suka sami dama.
Yadda kaddara da kiran jama’a ya ingiza Binani shiga siyasa
Ana alakanta shigan siyasan Binani akan kaddara da kuma kiran jama’a wadda wadannan abu biyun ne suka kaita ga wannan matakin duk kuwa da cewan hakan ya sabawa tunanin Dr. Ahmed Modibbo a tashin farko.
Kafin ta shiga siyasa, Binani ta kasance matashiyar yar kasuwa wacce ta sadaukar da dukiyanta akan jama’a. Saboda yadda take da burin taba rayuwar al’uma yasa ta bude wata gidauniya mai zaman kanta inda ta fara aikin tallafi a karkashinta a kananan hukumomin Yola ta arewa da ta kudu wadda sukafi kusa da ita.
Ta nan ne Binani ta sami daman tallafawa jama’a musamman ma iyalan da basuda galihu inda aka ga mata, matasa da masu larurar nakasa suka sami madogara tare da bata tallafin karatu wa marayu da sauran dalibai yan asalin jihan, gamida samar da motocin bada agajin gaggawa wa Musulmai da Kiristoci a kananan hukumomin.
Ire iren wadannan ayyukan ne ya janyo hankalin jama’a zuwa kanta wadda bayan mata fatan alheri suka kuma yi mata kira akan bukatar shiga siyasa domin ta samu daman tallafa musu sosai.
Inda batayi wata wata ba wurin turasu ga mai gidanta Dr. Modibbo wadda karara ya fito fili ya bayyana musu cewan matarsa batayi wannan aikin don a biyata ba kuma yaki yarda da bukatar tasu toh sai dai bayan matsa mishi lamba da jama’an sukayi daga karshe dai ya yarje mata da taje ta yiwa al’uma hidima.
Da farko dai jama’an turata sukayi zuwa majalisar wakilai inda ta wakilci kananan hukumomin Yola ta arewa Yola ta Kudu da Girei kuma mace ta farko data rike wannan matsayi, wadda bayan samu gamsasshen wakilci na gari daga gareta suka sake aikata zuwa majalisar dattawa.
Bayan aiwatar da aiki irin na madi ka ture a majalisar dattawan ne kuma jama’a suka sake ganin akwai bukatar su sake kiranta domin neman babbar kujeran shugabanci wadda hakan ne ya haifar da nasaran data samu a zaben fidda gwani na gwamna a jam’iyar APC inda ta kada abokan karawarta maza biyar wadda kuri’un da dukansu suka samu bai kai nata ba.
A bayyane yake cewa Binani bata taba neman wani kujeran siyasa don rajin kanta ba, a kulli yaumin jama’a ke mata kira shi yasa ta dabi’antu da dabi’an nan na cin zabe da gagarumin rinjaye saboda jama’an ne ke bukatarta ba akasin haka ba.
Babban dalilin da yasa jama’a suka yi mata kira data zo ta nemi kujeran gwamna shine yin la’akari da irin aikin kawo ci gaban kasa da tayi a majalisar dattawa. Duk da cewa ita sanata ce amma tana aiki tamkar wata gwamna inda akaga ta gina hanyoyi, asibitoci tona bohula, bada kayan tallafi wa dubbannin jama’a uwa uba shine kirkiro da dokoki wadda zai taimaki jama’an kasa baki daya.
A matsayinta na sanata ta mayar da Adamawa baki daya zuwa mazabarta inda jama’a daga Madagali zuwa Toungo zuwa Belel suka amfana da tallafin nata ta fannin koyon sana’o’i da dai sauransu wadda hakan ya taimaki iyalai da dama.
Wasu da dama na tunanin Binani tayi nasaran lashe zaben fidda gwani na gwamna ne saboda goyon bayan data samu daga mata, toh sai dai lamarin ba haka yake ba domin kuwa Binani tayi nasara ne saboda itace yar takara da tafi chanchanta da dacewa wacce ta samu goyon bayan maza da mata wadanda sukayi amannar cewa lokaci yagi da zasu biyata da irin tallafawa da take musu.
Tarihin nasararta zai sake maimaita kansa a zaben gomna dana yan majalisa dake tafe fiye ma dana zaben fidda gwani saboda yadda jama’a zasu fito kwansu da kwarkwatansu domin kada mata dimbin kuri’u sanadiyar kyawawan halayyarta na tausayi da tausayawa, a cewar Barata.
Toh sai dai a wani mataki na neman yabawa irin ta siyasa gomna Fintiri yayi wani yunkuri dake kama da kwafe irin ayyukan sanata Binani wadda nashi yafi kama da sayan kuri’u bayan dage zaben gomna dana yan majalisar jaha na ranar 11 ga watan maris da akayi.
A ranar talatan nan ne rahotanni suka nuna cewan gomnan ya rabawa mata 10,000 Naira dubu Hamsin Hamsin wadda hakan yasa masu fashin baki akan siyasa a jahar Adamawa suka soki lamirin gomnan bisa yadda ya nuna kwadayin sake komawa kan kujera karara ta hanyar sayan imanin jama’a.
Inda sukayi kira ga wadanda suka ci gajiyar shirin dasu karbi rabonsu amma su zabi wadda suke bukata a ranar zabe.
Sun tuna ko a baya ma yadda rashin tallafawa jama’a da gomnan baya yi yasa daya daga cikin makusantansa Hon. Umar ya shawarci gomnan da ya maida hankali wurin tallafawa jama’a domin saukaka musu wahalhalu da suke fiskanta inda daya daga cikin hadiman gomnan Sa’idu Sarki Zana yayi mishi barazana tare da shafa mishi kashin kaji saboda fadawa gomnan gaskiya da yayi inda ya tilastawa Umar janye kalamansa bisa dalilin rashin jin dadin kalaman da gomnan yayi.
Majiya daga gidan gomnatin ya tabbatar da cewa bayan dage zabe da INEC tayi daga ranar 11 ga watan maris zuwa 18 shine gomnan ya shirya wannan yaudaran da ya kira da sunan tallafi wa mata 10,000 toh sai dai bincike ya nuna cewa matan da sukaci gajiyar tallafin basu wuce 600 ba.
A bayyane yake cewa gomnan bai shirya aiwatar da wannan aikin tallafin ba amma da yake tallafin da sanata Binani keyi yana hanashi bacci, sai yayi amfani da dage zabe da akayi a matsayin wata kofa daya samu domin yaudaran iyayenmu mata ta hanyar yin karyan cewa zai tallafa musu da jarin 50,000.
A mahanga irin ta lissafi aikin tallafin baida wani tasiri kawai an shirya shi ne don yaudaran jama’a duba da yadda gomnatin bata da daman hada sunayen mata dubu goma a dan kankanin lokaci shi yasa aka gaggauta daukan sunayen matan wasu manya da yan uwansu, a cewar wani makusancin gomnatin.
Wani abu daya bayyana a matsayin tsoron guguwan sanata Binani da gomnan keji shine dakatar da ayyukan kungiyoyi masu zaman kansu bisa zargin za’a iya amfani dasu wurin sayan kuri’u, matakin, wadda dama anyi tsammanin daukansa yasa masu ruwa da tsaki a al’amuran yau da kullum bayyana cewan take hakkin jama’a ne da karfin gomnati.
Rahotanni sun kara bayyana cewan kokarin gomnan na dakatar da Binani shiga zabe ya gamu da cikas bisa yadda fannin shari’a tasa kafa ta shure bukatar gomnan.
Binani ta sami daman watayawa a fagen siyasan Adamawa ne sanadiyar fatan alheri da fatan nasara da jama’a ke mata bisa kyawawan dabi’unta.
Ta kasance mace ce mai karfin fafutukar nemowa jama’ar jaharta ayyukan ci gaba dana more rayuwa gamida samar da ingantattun dokoki wadda zasu kai kasan gaba.
An kiyasta cewan Binani ta tallafawa akalla mutum dubu dari wadda yayi sanadiyar cire yankuna da dama daga cikin kangin talauci kuma a shekaru hudu na baya bayan nan Binani a matsayinta na sanata tayi aiyukan ci gaba da gomna ne kadai zaiyi yunkurin aiwatarwa wadda ya taba rayukan al’uman Adamawa baki daya kuma hakan na daga cikin dalilan da yasa zataci zabe a Adamawa cikin ruwan sanyi, a cewar Barata.